in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan Ukraine za ta warware rikicin kasa bisa tsarin dokoki, in ji ma'aikatar harkokin wajen Sin
2014-02-25 20:30:30 cri
A halin yanzu, ana fuskantar mawuyacin hali a kasar Ukraine, inda wasu bangarorin da abin ya shafa a kasar ba su amince da sabuwar gwamnatin kasar ba. Kan lamarin, yau Talata 25 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a birnin Beijing cewa, kasar Sin na mai da hankali sosai kan abubuwan da suka faru da kuma za su faru a kasar Ukraine a nan gaba, kuma a ganin kasar Sin, ana ci gaba da kyautata yanayin da kasar Ukraine ke ciki bisa kokarin bangarorin daban daban da abin ya shafa, Sin na fatan za ta iya ciyar da yunkurin siyasa gaba wajen warware ricikin kasar bisa tsarin dokoki. Bugu da kari, kasar Sin tana son ci gaba da raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tare da kasar Ukraine bisa ka'idojin adalci da cimma moriyar juna. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China