in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan kasar Ukraine suna farautar tsohon Shugaba Victor Yanukovich
2014-02-25 14:38:32 cri

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Ukraine ta sanar da fara bin bahasin gwamnatin Victor Yanukovich a ranar 24 ga wata kan zargin da aka yi mata na nuna karfi wajen murkushe masu zanga-zanga fararen hula, tare kuma da samar da sammacin neman tsohon shugaban da manyan jami'ansa.

Mukadashin ministan harkokin cikin gida na kasar Ukraine Arsen Avakov ya sanar a wannan rana cewa, sassan da abin ya shafa sun fara bincike kan wannan batu tare da samar da sammacin cafke Victor Yanukovich da dai sauran manyan jami'ansa. A wannan rana kuma, ofishin yada labaru na hukumar zabe ta kasar ya sanar da shirin yin babban zaben kasar a ran 25 ga watan Mayu, kuma daga yau din nan Talata 25 ga wata ne za a fara gabatar da 'yan takarar da za su tsaya zaben..

An ba da labari cewa, firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev ya nuna cewa, in dai an dauki wadanda suka rufe fuskokinsu suka fito kan titi rike da bindiga a matsayin gwamnati, to, zai yi wuya kasarsa ta yi mu'ammala da irin wannan gwamnati. A sa'i daya kuma, kasar Rasha za ta aiwatar da dukkan yarjeniyoyin da ta daddale da kasar Ukraine.

Ban da haka, mai ba da shawara ga shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaron kasar Madam Susan Rice ta yi gargadi a ran 23 ga wata kan kasar Rasha cewa, kada ta dauki matakin soja kan halin da Ukraine ke ciki.

A nata bangaren kasar Sin ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajen ta Madam Hua Chunying ta bayyana a ran 24 ga wata cewa, kasar na dora babban muhimmanci kan halin siyasa na kasar Ukraine, kuma tana fatan bangarorin daban-daban cikin kasar za su yi shawarwari a siyasance cikin lumana domin daidaita bambancin ra'ayi, don tabbatar da zaman karko ta fannin siyasa, da kuma maido da zaman oda da doka a cikin al'umma. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China