Shugaban wucin gadi Turchinov ya jaddada cewa, kasar sa na cikin wani mawuyacin hali a fannin tattalin arziki, don haka ana fuskantar manyan matsaloli da suka kasance a hukumomin kudi da na banki da dai sauransu. Turchinov ya kuma bukaci jam'iyyu daban daban da su cimma ra'ayi daya nan da ranar Talata mai zuwa kan kafa rukunin da ya lashe yawancin kujerun majalisar dokoki, da kuma kafa gwamnatin hadin kan kasa baki daya.
Taron kuma ya kaddamar da jerin kudurori game da Yanukovich da manyan jami'an gwamnatinsa, ciki har da kwace gidajen sa na kasaita dake kusa da Kiev, babban birnin kasar, da sakin masu zanga-zanga dake adawa da gwamnati guda 64 daga gidan kaso, da dai sauransu.
Sai dai har yanzu ba a san inda Yanukovich yake ba. (Bilkisu)