Jiya 20 ga wata, an sake yin rikici a kusa da filin 'yancin kai dake birnin Keiv, hedkwatar kasar Ukraine.
Game da wannan batu madam Hua ta bayyana cewa, Sin ta damu sosai kan mutuwa da jikkatar mutane da dama sakamakon abkuwar rikicin, kuma ta yi Allah wadai da wannan danyen aiki na nuna karfi,tare da fatan bangarorin da abin ya shafa za su bayyana bukatunsu bisa dokoki kuma cikin lumana. Dadin dadawa, Sin ta yi kira da su yi hakuri, su daidaita matsaloli bisa dokoki bayan yin la'akari da kawo alheri ga jama'ar Ukraine da tabbatar da zaman lafiya a wannan yanki.
Madam Hua ta bayyana fatan kasar Sin ga kasashen duniya da su yi kokari tare da taka rawar a zo a gani wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar Ukraine.(Fatima)