A jiya Lahadi ne Aleksandr Turchinov, sabon shugaban majalisar dokokin kasar Ukraine ya ce, ya kamata Ukraine ta koma kan hanyar hada kai da kasashen Turai, tare da raya dangantaka a tsakaninta da kasar Rasha bisa ka'idar kafa kyakkyawar hulda a tsakanin makwabta.
Ya kara da cewa, yanzu tilas ne Ukraine ta gaggauta kawo karshen hargitsi a kasar, da maido da doka da oda, da kuma yaki da dukkan aikace-aikacen da za su kawo wa kasar baraka da lalata cikakkun yankunan kasar.
A wannan rana kuma, an yi tattaunawa a tsakanin shugabannin kasashen Rasha da Jamus, da kuma tsakanin shugabannin kasashen Faransa da Jamus dangane da halin da ake ciki a kasar ta Ukraine, inda suka jaddada cewa, dole ne a tabbatar da dinkuwar kasar ta Ukraine waje daya da cikakkun yankunan kasar. (Tasallah)