in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayar da sammacin kama Yanukovych
2014-02-24 20:40:14 cri
A yau Litinin ne shugaban rikon kwarya na kasar Ukraine, ya bayar da sammacin kama shugaba Viktor Yanukovych, bisa zargin aikata manyan laifuffuka kan masu bore a makon da aka kwashe ana zubar da jini a Kiev, babban birnin kasar.

Mai rikon mukamin ministan cikin gida na kasar Arsen Avakhov ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, an sanya sunan hambararren shugaban kasar da sauran jami'an kasar da dama cikin jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo a Ukraine, saboda laifin kashe jama'a, inda ya ce shugaba Yanukovich ya isa yankin Crimea ne a daren ranar Lahadi.

Rahotanni na cewa, Yanukovich ya bar kasar ce ranar Jumma'a ta wani jirgi mai saukar ungulu, bayan sanya hannu kan wata yarjejeniya da 'yan adawa da nufin kawo karshen tashin hankalin kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China