Bayan cimma yarjejeniyar, majalisar dokokin kasar ta Ukraine ta zartas da kudurin dokar maido da kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 2004.
Bisa sanarwar da ofishin shugaban kasar ta Ukraine ya fitar, cikin awoyi 48 bayan daddale yarjejeniyar, za a zartas, a rattaba hannu, tare da gabatar da wata doka ta musamman, wadda za ta tabbatar da maido da kundin tsarin mulkin na shekarar 2004.
Har wa yau bangarorin biyu, za su kafa majalisar dokoki ta hadin gwiwa cikin kwanaki 10. Dadin dadawa, yarjejeniyar ta tanadi yin kwaskwarima, ga kundin tsarin mulkin kasar, wanda za a yi nan da watan Satumbar dake tafe, a kokarin daidaita ikon da shugaba da gwamnati, da kuma majalisar dokokin kasar ke da shi.
Hakazalika an amince da gudanar da babban zaben kasar ya zuwa watan Disambar bana. Kuma mahukuntan kasar ba za su sanya dokar ta baci ba, su kuma kauracewa nuna karfi. Su kuma 'yan adawa za su mika makaman su, ga hukumar kula da harkokin cikin gidan kasar cikin sa'oi 24, bayan tabbatar da kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 2004,
Ana sa ran bangarorin biyu, za su dauki matakan tabbatar da zaman lafiya a kasar, ta hanyar kauracewa mamaye gine-ginen gwamnati, da dakatar da kafa shingaye kan tituna, da wurare ziyarar 'yan yawon shakatawa da kuma filayen taruka.
Bugu da kari mahukuntan kasar, da 'yan adawa, da kuma majalisar kasashen Turai, zasu gudanar da bincike, kan zargin amfani da karfi yayin tarzomar da ta gudana.(Fatima)