in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar dokokin Ukraine ya yi murabus
2014-02-23 17:35:56 cri
Bayan da shugaban kasar Ukraine ya sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da kungiyar adawa ta kasar don warware rikicin siyasa kasar, a halin yanzu, ana samun kwanciyar hankali a kasar. Kwanan baya, kungiyar adawa ta kasar Ukraine ta yi kokarin zartas da wasu kudurori da dokoki ta majalisar dokokin kasar, don cimma bukatunta. Kana, a ran 22 ga wata, shugaban majalisar dokokin kasar ya sanar da yin murabus.

Bisa bayanin da ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Ukraine ta bayar, an ce, ya zuwa yanzu, mutane 77 sun rasu a sanadiyyar rikice-rikicen da aka tayar tun ranar 18 ga wata, yayin da mutane da dama suka jikkata. An kebe kwanaki biyu na karshen makon, a matsayin ranakun zaman makoki a duk fadin kasar ta Ukraine.

Kafofin watsa labaran wurin sun ruwaito wani mai ba da shawara ga shugaban kasar na cewa, a halin yanzu, shugaban kasa Viktor Yanukovich yana ziyarar aiki ne a birnin Kharkov dake gabashin kasar. Zai sa hannu kan dokokin da majalisar dokokin kasar ta zartas da su kwanan baya, kana zai gana da masu kada kuri'u, zai kuma yi jawabi ta talebijin da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China