Rahotanni daga birnin Geneva, na cewa wakilan gwamnatin kasar Sham da na kungiyoyin 'yan adawar kasar, sun gaza cimma wata matsaya, yayin shawarwari a zagaye na biyu da suka gudanar a jiya Jumma'a.
A ranar Alhamis 13 ga wata ne dai wakilin musamman na MDD, da kawancen kasashen Larabawa AL, mai kula da rikicin kasar ta Sham Lakhdar Brahimi, ya gana da mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka Wendy Sherman, da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Gennady Gatilov a birnin na Geneva, da zummar sa kaimi ga shawarwarin da bangarorin biyu ke aiwatarwa a wanna karo. Sai dai har kawo ranar 14 ga wata, bangaorin biyu sun ci gaba da zargin juna, kuma ba su kai ga samun wani ci gaba a shawarwarin da suke yi ba.
Har wa yau a dai ranar ta Jumma'a, Mr. Brahimi ya gana da wasu jami'an gwamnatin kasar ta Sham, da wakilan kungiyoyin adawa. Yayin wannan ganawa mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sham Faisal Makdad, ya bayyana takaicinsa game da sakamakon shawarwarin. Ya ce, gwamnatin Sham, na fatan kawo karshen rikicin kasar ta hanyar siyasa, kuma kamata ya yi tun da farko a tattauna batun kawo karshen yin amfani da karfin tuwo, da yaki da ta'addanci a gun taron, maimakon batun kafa hukumomin wucin gadi, da 'yan adawa ke baiwa muhimmanci.
Shi ma a nasa tsokaci kakakin tsagin 'yan adawa ya amince da cewa, yanzu haka ana cikin halin kaka-nika-yi. Ya ce kungiyar ta bayyanawa Brahimi, wata manufa ta kafa hukumar wucin gadi a ranar Alhamis 13 ga wata, da fatan tsagin gwamnati zai mayar da martanin da ya dace, game da manufar da aka sanya gaba, ta warware rikicin kasar bisa turbar siyasa. (Amina)