Kungiyar kasa da kasa mai zaman kanta a game da sa ido kan lamuran shari'a da kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ita ce ta sanar da hakan a ranar Laraba a birnin Dakar na kasar ta Senegal, cikin rahoton ta na wannan shekara ta 2012.
A cikin wannan rahoto kungiyar Amnesty International ta sanar da cewa, mutane 22 ne suka mutu sanadiyyar azabar da jami'an tsaro suka yi musu a cikin shekaru 12 na tsawon mulkin shugaba Abdoulaye Wade.
A cikin wannan rahoto, an nuna bukatar a gurfanar tare da hukunta wadanda suka yi azaba ga mutanen. Amnesty International ta nemi da a kawo kwaskwarima ga dokokin gudanar da shari'a kan wadanda suka yi laifi kan azabtar da jama'a.An girka hukumar sa ido a wuraren da ake tsare jama'a masu laifi, sai dai har yanzu hukumar za ta samu isashen kayayyakin aiki ba domin ta gudanar da aikinta yadda ya kamata. An ce, kamata ya yi gwamnati ta nuna cewa, da gaske ta ke yi wajen kokowa da lamarin azabtar da jama'a, ta hanyar bayar da kayan aiki ga wannan hukuma.(Abdou Halilou)