Tashin hankalin ya bar wassu mutane 300 daga bangarori biyu dake arangama da juna dukkan su da raunuka a lokacin da ma'aikatar ta fitar da bayani.
Sai dai kuma ma'aikatar ta kuma tabbatar da cewar 'yan sanda 9 sun mutu a cikin sannan kuma wassu 371 sun samu raunuka.
Zanga zangar nuna kin jinin gwamnati da ake yi a Kiev ya koma tashin hankali mai tsanani a safiyar talatan nan lokacin da wassu masu tsatsauran ra'ayi suka kai hari ma 'yan sanda da abin tartsatsin wuta da kuma bam din da akan shirya shi hade da man fetur.(Fatimah Jibril)