in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gamayyar kasa da kasa sun mai da hankali sosai kan rikice-rikicen da ke faruwa a Ukraine
2014-02-19 11:40:38 cri

Arangamar da aka yi tsakanin 'yan sandan kasar Ukraine da masu zanga-zanga a ran 18 ga wata, wadanda suka haddasa jikkata tare da mutuwar daruruwan mutane, sun janyo hankulan gamayyar kasa da kasa sosai.

A ran 18 ga wata da safe ne, dubban masu zanga-zanga suka tashe daga dandalin 'yancin kai dake tsakiyar babban birnin kasar, Kiev, zuwa babban ginin majalisar dokokin kasa don yin kira ga majalisar dokokin kasar da ta maido da kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 2004. Daga bisani kuma, rikice-rikice masu tsanani tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda suka kaure, har zuwa daddaren wannan rana. Kuma bisa labarin da aka samu daga hukumar kula da harkokin cikin gida ta kasar Ukraine, an ce, ya zuwa tsakiyar daren wannan rana, rikice-rikice sun haddasa mutuwar mutane guda 18, masu zanga-zanga sama da 200 suka jikkata, yayin da 'yan sanda sama da 300 suka ji rauni.

A wannan rana kuma, ta bakin kakakinsa babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya sake jaddada cewa, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su kwantar da hankulansu, ya kuma yi kira da su koma teburin shawarwari.

Bugu da kari, kungiyar tarayyar kasashen Turai, hukumar kula da yarjejeniyar arewacin tekun Atlantika da kasashen Burtaniya da kuma Faransa da sauran kasashe sun ba da sanarwa, inda suka nuna damuwarsu game da yanayin na kasar Ukraine.

A wannan rana kuma, ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta ba da wata sanarwa, inda ta bayyana cewa, tsoma bakin wasu 'yan siyasa na yammacin kasashe da wasu hukumomin kasasen Turai ta haddasa ci gaba na rikice-rikice a birnin Kiev na kasar Ukraine, sanarwar ta kuma yi kira ga kungiyar adawa ta kasar Ukraine da ta tsayar da aikace-aikacenta, ta yadda za ta fara yin shawarwari tare da gwamnatin kasar yadda ya kamata, ta yadda za a samar da kwanciyar hankali a kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China