Shugaban kasar Sudan, kuma jagoran jam'iyyar NCP dake mulkin kasar, Omar al-Bashir ya yi kira ga shugabannin jam'iyyu daban-daban da su ba da kulawa ga shawarwari tsakanin bangarorin daban-daban na kasar yayin da ya gana da su a jiya Litinin 27 ga wata, domin a mai da hankali kan tabbatar da zaman lafiya, kyautata tattalin arzikin kasar, ba da tabbaci ga tsarin mulkin kasar da sa kaimi ga samun zaman jituwa tsakanin al'umma.
A sa'i daya kuma, Mr Al-Bashir ya sanar da shirin yin kwaskwarima kan harkokin kasar da jam'iyyarsa ta tsara. A nata bangaren, jam'iyyar adawa dai ta ki karbar goron gayyatar wannan ganawa tare da shugaba Al-Bashar, da take zargi da tura kasar Sudan cikin mawuyacin hali da kasa kubutar da kasar daga cikin matsalolin da take fuskanta. (Amina)