Aguer ya ce, akwai mutane kimanin 200 zuwa 300 ke cikin jirgin, cikinsu har da mata da yara, a lokacin, wadannan mutane sun bar birnin Malakal ne inda fada ya barke na baya bayan nan ta jirgin ruwa, kuma kamar yadda bayanai suka nuna jirgin yana da karfin daukan mutane 80 kawai, amma domin tsere ma tashe tashen hankulla da ake a garin, mutane da dama suka rika rige-rigen shiga jirgin.
Majiyar labarin ta ce, mutane kalilan ne kawai suka samu damar iyo zuwa gabar kogin don tsirar da rayukan su bayan nutsewar jirgin.
Tuni, kafofin yada labaru suka bayyana cewa, bayan da fada ya barke a kasar Sudan ta Kudu, ya zuwa yanzu mutane sama da dubu 50 sun tsere daga kasar zuwa wassu kasashe makwabta wato kamar Uganda duk da dai ba a tabbatar da ainihin yawan su ba tukuna.
Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta Uganda ta ce, kasar ta riga ta karki 'yan gudun hijira na Sudan ta Kudu da yawansu ya kai dubu 46.(Bako)