A wannan rana, jami'in kula da harkokin jin kai na MDD da ke kasar Sudan ta Kudu, ya ba da wata sanarwa inda ya nuna cewa, a halin yanzu, hukumomin ba da taimakon jin kai sun himmatu wajen gudanar da ayyukansu a kasar, inda suka samar da abinci, kayyayakin agaji da kuma ayyukan jinya da dai sauransu, kuma suna karfafa ayyukansu wajen samar da karin ruwa mai tsabta da kuma bayan gida. Don haka, ya kamata bangarorin daban daban da abin ya shafa, su tabbatar da samar da tsaro ga hukumomin ba da taimakon jin kai a kasar Sudan ta Kudu, tare da girmama ayyukansu, da kare ma'aikatansu da kuma kadarorinsu. (Maryam)