A cikin sanarwar, an ce, Ban ki-moon shi ma ya nuna damuwa game da kalubalen da ake fuskanta wajen bada agajin jin kai, a sa'i daya kuma, ya yi Allah-wadai da yadda wasu mayaka suke kwatan motocin ba da agajin jin kai, da satar abinci da kayayyaki da kakkausan murya.
Ban da wannan kuma, Ban ki-moon ya yi kira ga bangarorin da rikicin kasar Sudan ta Kudu ya shafa da su tsagaita bude wuta nan take, don tashi tsaye wajen shiga yunkurin shawarwari karkashin shugabancin kungiyar raya gwamnatocin kasashe a yankin gabashin Afrika, don gaggauta magance mutuwar mutane da jikkatar wadansu, da kuma bin dokokin kasa da kasa.
Mr Ban daga nan sai ya sake nanata cewa, za a hukunta wadanda suka hallaka fararen hula da masu aikin jin kai da ma'aikatan M.D.D.bayan da aka kama su sannan kuma M.D.D. za ta ci gaba da kare jama'a.(Bako)