in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan gudun hijira fiye da dubu 30 sun tsere daga Sudan ta Kudu zuwa kasashe makwabta
2014-01-08 10:59:07 cri

Hukumar da ke kula da harkokin 'yan gudan hijira ta MDD ta bayyana a ran 7 ga wata a birnin Geneva cewa, tun bayan barkewar rikici a Sudan ta Kudu a tsakiyar watan jiya, 'yan gudun hijiirar kasar fiye da dubu 30 sun tsere zuwa Uganda, da Habasha, da Kenya, da Sudan da dai sauran kasashen da ke makwabataka da kasar.

Kakakin hukumar Madam Melissa Fleming ta bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya a Geneva cewa, ya zuwa ranar 6 ga wata, 'yan gudun hijira fiye da dubu 23 sun tsere daga Sudan ta Kudu zuwa Uganda, a halin yanzu dai yawancin 'yan gudan hijirar suna zama a wasu cibiyoyin da ke arewa maso yammacin kasar Uganda, inda za su iyar tafiyar da zaman rayuwarsu na yau da kullum.

Madam Fleming ta kara da cewa, Habasha ta riga ta karbi 'yan gudun hijira fiye da 5300 daga Sudan ta Kudu, Kenya ta karbi 3200. Ban da wannan kuma, 'yan gudun hijira masu yawa sun shiga cikin kasar Sudan, yanzu hukumar da ke kula da harkokin 'yan gudan hijira ta MDD tana kokarin tabbatar da yawan adadinsu.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China