A cewar kakakin majalisar Martin Nesirky a zantawar da ya yi da manema labarai a Talatan nan, an ce, an yi amfani da manyan bindigogi da motocin yaki wajen wannan arangama da aka fara shi da sanyin safiyar ranar a kusa da sansanin majalisar dake Malakal a jihar Upper Nile dake Sudan ta Kudu.
Wasu harsasai da aka harba ta ko ina sun fada a cikin sansanin tare da jikkata wadansu mutane dake sansanin don gudun hijira, yanzu haka, in ji shi, tawagar UNMISS na ba da magani ga wadanda wannan tsautsayi ya rutsa da su da dama a asibitinta.
A bayanin da tawagar ta yi, fadan yanzu ya sa adadin wadanda suka rasa muhallinsu ya kusa ninka wadanda ake da su a sansanin da kusan 20,000, abin da ya sa ma'aikatan wanzar da zaman lafiya kusan 1,000 ke kula da su, gaba daya kuma ma'aikatan wanzar da zaman lafiyan na kula da wadanda ke sansanoninsu 65,000 a fadin kasar.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR ta yi kiyasin cewa, kusan 'yan gudun hijira 78,000 ne suka tsere daga kasar zuwa kasashe makwabtansu kamar Uganda, Habasha da Kenya tun lokacin da fadan ya barke a tsakiyar watan jiya na Disamba tsakanin sojojin gwamnatin Salva Kiir Mayardit da na magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.
Fadace-fadace dai a wannan sabuwar kasar ya zuwa yanzu sun riga sun yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 1,000. (Fatimah)