in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarorin biyu da rikicin Sudan ta Kudu ya shafa sun daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta
2014-01-24 10:51:28 cri
Bayan da aka yi shawarwari har na tsawon kwanaki 20,daga karshe a ranar 23 ga wata da dare, wakilan bangarorin biyu da rikicin Sudan ta Kudu ya shafa sun daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Wakilin gwamnatin Sudan ta Kudu Nhial Deng Nhial a shawarwarin da kuma takwaransa a bangaren dakarun 'yan adawa na kasar Taban Deng Gai sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar.

Tun a tsakiyar watan Disamba na bara ne, rikici ya barke tsakanin gwamnatin Sudan ta Kudu da dakarun da ke adawa da gwamnatin, kungiyar raya gwamnatocin kasashen gabashin Afrika wato IGAD ta dukufa ka'in da na'in wajen yin sulhu a tsakanin bangarorin biyu, kuma tana fatan ganin bangarorin biyu za su daddale yarjejeniya don kawo karshen rikici a tsakaninsu.

Bisa ga shiga tsakani da kungiyar IGAD ta yi, a ranar 4 ga wata, wakilan bangarorin biyu da rikicin Sudan ta Kudu ya shafa sun fara yin shawarwari a birnin Addis Ababa hedkwatar kasar Habasha. Mai shiga tsakani na kungiyar IGAD kuma tsohon ministan harkokin wajen kasar Seyoum Mesfin ya bayyana cewa, bayan da aka yi shawarwari har na tsawon makwanni 3, a ranar 23 ga wata, an cimma nasarar daddale yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu na Sudan ta Kudu game da tsagaita bude wuta da sakin fursononin siyasa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China