Ya ce, cikin 'yan makwanni masu zuwa, kasar za ta aike da sojoji guda 350 wadanda a halin yanzu ke zaune a kasar Cote d'ivoire zuwa kasar Sudan ta Kudu, don gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya na MDD. Kuma bayan watanni uku, kasar Ghana za ta aike da sojoji guda 850 zuwa kasar Sudan ta Kudu, yayin da wadannan guda 350 da ta tura zuwa kasar Sudan ta Kudu da farko za su koma gida.
Tun lokacin da ta samu 'yancin kai a shekarar 1957, kasar Ghana ta sha halartar ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, kungiyar tarayyar kasashen Afirka da kuma na gamayyar tattalin arziki ta yammacin kasashen Afirka. (Maryam)