Ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS ya kira taron tattaunawa kan yadda za a kafa kwamitin tsaron kasar
Ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya kira wani taro a Juma'a nan 24 ga wata a nan birnin Beijing, domin tattaunawa tare da yanke shawara kan yadda za a kafa wani kwamitin tsaro kasa na tsakiya. Inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron.
Yayin taron, an yanke shawarar nada Xi Jinping da ya zama shugaban kwamitin tsaron, haka kuma Li Keqiang, Zhang Dejiang zasu kasance mataimakan shugaban, ban da haka akwai zaunannen wakilai da wasu wakilai da dama.
A matsayin wata hukuma mai tsara shiri da daidaita harkokin tsaron kasar, kwamitin zai daidaita da ba da kulawa ga wasu manyan batutuwan da suka shafi tsaron kasar. (Amina)