in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar JKS ya bukaci a yi kokarin kawar da cin hanci da rashawa a kasar Sin
2014-01-19 17:25:35 cri
Kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya ba da wata sanarwa a ranar Lahadi 19 ga wata, inda ya bukaci sassan kwamitin da su yi kokarin bin jawabin da shugaban kasar kuma babban magatakardan jam'iyyar JKS, mista Xi Jinping, ya yi a wajen wani taron kwamitin ladabtarwar, cewa kamata ya yi a kara zurfafa gyare-gyare don ci gaba da kawar da cin hanci da rashawa a kasar, da kokarin tabbatar da da'a tsakanin mambobin jam'iyyar, don samun amincewar jama'a.

Sanarwar ta ce, yayin da shugaba Xi yake jawabi, ya waiwayi nasarorin da aka samu a shekarar da ta wuce a kokarin yaki da cin hanci da rashawa, sa'an nan ya yi bayani kan shirin da aka tsara da manyan ayyukan da za a yi a nan gaba, inda kalamansa suka bada kwarin gwiwa ga 'yan jam'iyyar JKS a fannin tabbatar da da'a da kokarin kawar da cin hanci da rashawa, matakin da zai kara karfafa matsayin jam'iyyar wajen jagorantar aikin raya zaman gurguzu bisa yanayin musamman na kasar Sin. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China