Wani masani a fannin manyan manufofin tattalin arziki, dake cibiyar tattara bayyanai ta kasar Sin Wang Yuanhong, ya bayyana a ran 12 ga wata a nan birnin Beijing cewa, tsarin daidaita harkokin al'umma, da cikakken zama karo na uku na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin a karo na sha takwas ya gabatar, ya shafi fannoni daban-daban, ciki hadda tattalin arziki, da siyasa, da zamantakewar al'umma da dai sauransu.
An rufe cikakken zaman na wannan karo a ran 12 ga wata a nan birnin Beijing, tare kuma da ba da sanarwa kan zurfafa gudanar da kwaskwarima a dukkan fannoni.
Cikin tsokacin nasa, Wang Yuanhong ya furta cewa, ga misalin tattalin arziki, tsare-tsare daban daban sun hade sun zama wani babban tsarin bai daya, wadannan tsare-tsare sun hada da tsarin hada-hadar kudi, da manufofin hada-hadar kudi, da kuma manufar ba da tabbaci ga zamantakewar al'umma. Kwaskwarimar da aka yi a wadannan fannoni, ba ma kawai za ta yi amfani wajen kawar da illa da take kawo cikas ga samun bunkasa ba ne, a'a har ma za ta samar da tushe mai kyau na karfafa daidaita harkokin kasa.
Game da matakan da sabuwar gwamnati za ta dauka wajen sauya hanyar samun bunkasuwar tattalin arziki a nan gaba kadan, Wang Yuanhong ya bayyana cewa, wannan ya danganta da tsari da karfin daidaita harkokin. Ya kara da cewa, gwamnati za ta ci gaba da habaka zuba jari, wato batun ba da damar zuba jari a kowane fanni ba tare da samun tarnaki daga gwamnati ba.
Ya ce wannan mataki ya bambanta sosai daga matakin da Sin ta taba dauka a da. Kwaskwarima da Sin ta yi a fannin sarrafa kayayyaki ya kusan kammala, ko da yake akwai koma bayan a wasu fannoni, ciki hadda kudin ruwa, da darajar kudi, da kasuwar kudade da sauransu, don haka Sin za ta mai da hankali kan wadannan fannoni a nan gaba. (Amina)