Rahoton ya ce, babban makasudin zurfafa gyare-gyare a dukkan fannoni shi ne, domin kyautata da bunkasa tsarin gurguzu da ke da sigar musamman irin ta kasar Sin, da sa kaimi ga kafuwar tsari na zamani wajen tafiyar da harkokin kasa da kuma inganta kwarewar gwamnati da ta dace da abubuwa na zamani. Tattalin arziki irin na gwamnati da kuma wanda a na gwamnati ba, dukkansu sun kasance muhimman sassa a tattalin arziki irin na kasuwanci da kuma na gurguzu, kuma dukkansu sun zama tushe mai muhimmanci wajen raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin.
Rahoton ya ci gaba da cewa, ya zuwa shekara ta 2020, za a samu kyakkyawan sakamako mai amfani a manyan fannoni, da kafa wani cikakken tsari mai amfani, wanda ake iya tafiyar da shi yadda ya kamata, ta yadda za a iya tabbatar da nagartattun tsare-tsare a fannoni daban daban.(Danladi)