Yayin da yake magana kan shirin yin kwaskwarima a dukkan fannoni da aka gabatar a gun cikakken zaman taro karo na 3, na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18, mista Zhou Tianyong ya bayyana cewa, a cikin shirin akwai abubuwa guda uku da ke daukar hankalinmu, da wasu karin batutuwa masu sarkakiya guda uku.
Da farko, akwai wani cikakken shiri na daidaita dukkan fannoni. Na biyu, wannan shiri ne da zai dauki dogon lokaci, wanda zai iya shafe shekaru a kalla bakwai. Na uku, dukkanin batutuwan na da sarkakiya babba da suke fuskanta a yanzu.
Game da wadancan abubuwa masu sarkakiya, Zhou Tianyong ya ce, da farko ana fuskantar tirjiya wajen yin kwaskwarima, wanda sau da yawa babban sakatare, da firaminista suka yi shelar kawar da wasu matakai ko shinge dake kiyaye moriyar wasu mutane. Na biyu, a yayin taron, an gabatar da daga matsayin bude kofa ga kasashen waje, ta yadda zai kai zuwa matsayin wasu tsare-tsare na duniya. Na uku, kamata ya yi a bude tunanin jama'a wajen yin kwaskwarima, tare kuma da samun ra'ayi daya kan sanarwar da taron ya bayar, da kudurin da kwamitin tsakiya ya tsaida.
Game da batun yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki kuwa, Zhou Tianyong ya nuna cewa, "abin da ya fi muhimmanci shi ne daidaita dangantakar dake tsakanin gwamnati da kasuwa, kana da sanya kasuwa ta kara taka rawar data dace." Zhou ya ce, batun da aka samu ci gaban sa a cikin shirin, shi ne yin amfani da kalmar "karfin yin takara" wajen raya tattalin arzikin da gwamnati ke sa ido a kansa, wanda ba a taba amfani da ita ba a da. Na biyu, an gabatar da batun kara inganta tattalin arziki a sassan da ba na gwamnati ba. Bugu da kari, za a kafa tsarin kiyaye ikon mallakar ilmi, a kuma karo na farko, aka gabatar da kalmar "gaurayayyen tsarin tattalin arziki ", wato watakila nan gaba, za a shigar da hannun jarin sassan da ba na gwamnati ba, cikin masana'antun gwamnati.
Bayan haka kuma, akwai batun kafa hadaddiyar kasuwa ta birane da kauyuka, wajen amfani da filayen gine-gine, da daukar matakai daga manyan fannoni ta hanyar kimiyya, da kafa wani tsari mafi budewa ga kasashen waje, dukkansu muhimman abubuwa ne a yayin taron. (Bilkisu)