in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gaggauta sa kaimi ga zamanantar da tsarin tafiyar da harkokin gwamnati, da kuma kafa tsarin kare muhalli
2013-11-16 16:25:36 cri

A ran 12 ga wata, Farfesa Song Shiming na sashen nazarin harkokin jama'a na makarantar koyon ilmin tafiyar da harkokin gwamnati ta kasar Sin, ya yi nuni game da ra'ayin da aka bayar a cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18, bisa gayyatar da aka yi masa, yana mai cewa, yin gyare-gyare kan tsarin tafiyar da harkokin gwamnati zai zama wani muhimmin sashe yayin ake yin gyare-gyare kan tsarin siyasa. Har ila yau yin gyare-gyare kan tsarin kare muhalli, zai zama wani abu da ya dace a gaggauta aiwatarwa ba tare da wani jinkiri ba.

Mista Song ya ce, a gun cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18, an gabatar da cewa, ya kamata a kiyaye martabar tsarin mulkin kasa, da tabbatar da tafiyar da ikon yanke hukunci, da bin bahasi cikin 'yanci, da kuma kyautata tsarin tabbatar da hakkin dan Adam. Ya ce lallai wadannan abubuwa sun jawo hankulan jama'a a gun taron, dangane da yin gyare-gyare kan tsarin siyasa. Mista Song ya kara da cewa, yin gyare-gyare kan tsarin tafiyar da harkokin gwamnati zai zama wani muhimmin sashe yayin da ake gyare-gyare kan tsarin siyasa. Abun da ya fi muhimmanci dangane da yin gyare-gyare ga tsarin tafiyar da harkokin gwamnati shi ne, kyautata ayyukan da gwamnati ke yi, don sa kaimi ga zamanintar da tsarin tafiyar da harkokin kasa, da samar da kwarewa a zamanance don tafiyar da harkokin kasa.

Song yana ganin cewa, da farko dai, kamata ya yi a baiwa amfani da ayyukan hukuma dama ta kiyaye adalci a zaman al'umma, da kago wani yanayi mai kyau ga bunkasuwa, da kuma ba da hidima mai inganci. Game da aikin sabunta hanyoyin da ake bi wajen tafiyar da harkokin gwamnati, Mista Song ya fadi cewa, ya dace a tanadi ayyuka, da matakai, da ajanda, dangane da iko cikin dokoki, matakin da zai zama wani muhimmin aiki yayin da ake yin gyare-gyare kan tsarin tafiyar da harkokin gwamnati. Ya kuma kara da cewa, sannu a hankali aikin gwamnatin kasar Sin, ya canza daga tafiyar da harkokin jama'a, zuwa kula da harkokin ba da hidima ga jama'a.

Da ya tabo batu kan kafa wani cikakken tsarin kare muhalli, bisa ga wani tsarin da aka tattauna a cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18, Mista Song Shiming ya bayyana cewa, don cimma burin kare muhallin halittu, da kyautata tsarin kare muhallin, kafa wani babban tsari don kare muhallin ya zama wani matakin da ya dace a gaggauta aiwatarwa.

Ya ci gaba da cewa, kare muhallin halittu wani batu ne na siyasa, wanda yake shafar zaman rayuwar jama'a, tare da kimiyya da fasaha.

Song yana ganin cewa, idan har ana son yin gyare-gyare kan tsarin kare muhalli, ya kamata a dauki matakai da dama, ciki had da abubuwa biyu mafiya muhimmanci. Na farko, ya kamta a kafa dokoki, na biyu, gwamnati ta tsara ayyuka don sulhunta bangarori daban daban da abin ya shafa.

Tuni dai aka rufe cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18 a ranar 12 ga watan Nuwamba, a gun taron an dudduba tare da zartas da takardar shawara da kwamitin tsakiya na JKS ya tattauna kan wasu manyan batutuwa.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China