Bisa labarin da aka samu daga jaridar Washington Post ta Amurka, an ce, shugabannin kasar Sin sun yi alkawarin kyautata ayyukan gwamnatin kasar, ta yadda kasuwanni za su ba da taimako mai kudurarren amfani wajen rabon arzikin kasa. Kuma don inganta harkokin yin gyare-gyare a kasa, jam'iyyar kwaminis ta Sin, ta kafa wata tawagar shugabancin harkokin gyare-gyare a dukkan fannoni, lamarin ya nuna cewa, aiwatar da gyare-gyare a kasar Sin zai zama wani muhimmin aiki mai nauyi kuma cikin dogon lokaci.
Ita kuwa jaridar Mainichi Shimbun ta kasar Japan ta yi sharhin cewa, Sin ta jaddada aniyarta ta raya tattalin arziki yadda ya kamata, da kuma mai da hankali kan amfanin kasuwanni cikin harkokin rabon arzikin kasa. Watau a nan gaba, kasar Sin za ta raya tattalin arzikinta ta hanyoyin bude kofa ga kamfanonin ketare, da bunkasa kamfanoni masu cin gashin kansu a gida, da kuma samar da sabbin guraben aikin yi a kasa da dai sauransu.
Wani masanin tattalin arziki na bankin 'yan asalin kasar Sin dake zaune a kasar Singapore Xie Dongming, ya bayyana cewa akwai harkoki guda biyar, wadanda ke janyo hankulan jama'a, a sanarwar cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18 da Sin ta fidda.
Da farko dai akwai batun cewa a nan gaba, za a gudanar da harkokin rabon arziki bisa bukatun kasuwanni. Na biyu, Sin ta kafa wata tawagar shugabannin kula da harkokin karfafa gyare-gyare a kasa, lamarin ya nuna aniyar kasar wajen yin gyare-gyare a cikin gida. Na uku kuma, Sin ta fara gyare-gyare kan fannin sha'anin kudi. Na hudu, gyare-gyare kan harkokin kasa za su amfana ga manoma sosai. Na biyar kuwa shi ne, gyare-gyare kan harkokin shari'ar kasa za su tabbatar da yanayin adalci a kasa ta Sin.
A sa'i daya kuma, wasu masanan ketare sun kuma ba da shawarwari ga kasar Sin kan hanyoyin neman bunkasuwar ta a nan gaba. (Maryam)