in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a daidaita ayyukan gwamnatin kasar Sin domin ba da damar yin amfani da tsarin kasuwa yadda ya kamata
2013-11-15 14:20:28 cri
Manazarci na hukumar nazarin manyan manufofin tattalin arziki na cibiyar binciken samun bunkasuwa na majalisar gudanarwa ta kasar Sin Zhang Liqun ya bayyana a ran 13 ga wata a nan birnin Beijing cewa, sharadin da aka sa a gaba wajen yin amfani da tsarin kasuwa a cikin aikin rarraba kayayyaki da kudade shi ne, daidaita ayyukan gwamnatin, wato gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata, kada ta sa hannu kn kome da kome.

An rufe cikakken zaman na wannan karo a ran 12 ga wata a nan birnin Beijing, inda aka bayar da sanarwa kan yadda za a zurfafa yin kwaskwarima a dukkan fannoni. A ganin Zhang Liqun, babban burin da aka gabatar a cikin sanarwa na da kyau sosai kuma bisa tsari, hakan ya sa an shiga wani muhimmin lokaci na samun ci gaba na kwaskwarimar da ake gudanarwa. Kudurin da aka gabatar a cikin taron ya yi kyau sosai, kuma an hada dukkan kwaskwarima da aka yi tare, da suka hada da kwaskwarima da aka yi a fannin tsarin tattalin arziki da siyasa, aka kuma hada da kyautata tsarin kasuwa da daidaita ayyukan gwamnati yayin da ake yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki. A sa'i daya kuma, an mai da hankali kan hakikanin matakan da za a dauka a cikin kwaskwarima da kuma gabatar da wasu manyan abubuwa da za a yi a cikin wannan aiki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China