Pan Jiahua, shugaban cibiyar nazarin ilmin bunkasuwar birni da muhallin birni ta kwalejin nazarin ilmin zaman al'ummar kasar Sin yana ganin cewa, kudurin kwamitin tsakiya na JKS game da muhimman batutuwan da suka shafi zurfafa ayyukan yin kwaskwarima a gida a dukkan fannoni wanda aka zartas a yayin cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18, ya ba da amsa mai kyau, ya biya burin al'umma, ya kuma dace da yadda ake zato.
Dangane da yadda za a kiyaye muhalli, a ganin Pan Jiahua, an kai ga cimma wannan kuduri, inda aka jaddada muhimmancin ayyukan kafa tsare-tsare kan hanyoyin inganta muhalli, haka kuma an shigar da tsare-tsaren hanyoyin inganta muhalli a matsayin wani muhimmin bangare cikin takardun da aka zartas da su a yayin cikakken zaman taro na uku na kwamitin tsakiya na JKS karo na 18, tare da gabatar da batun ware wasu muhimman yankunan musamman na kiyaye muhalli. Sakamakon karancin albarkatu da gurbata muhalli a nan kasar Sin, hakan ya kawo cikas da illa ga zaman rayuwar jama'a da bunkasuwar kasar. Sabili da haka ware wasu muhimman yankunan musamman na kiyaye muhalli na da muhimmanci matuka.
Ban da haka kuma, a cikin wannan kuduri, an sake nanata yin kwaskwarima ga tsarin kula da muhallin halittu. A ganin mista Pan, ya kamata a ci gaba da tabbatar da ganin kasuwanni sun taka muhimmiyar rawa wajen rarraba albarkatu. Kana kuma ya kamata a kyautata da inganta rawar gwamnatin kasar. Har wa yau kuma, ya zama dole a tsara doka da tsari da kuma ka'idoji masu amfani, in ba haka ba, kasuwanni da gwamnatin ba za su iya taka rawar da ta dace ba.(Tasallah)