A wannan rana ne kuma, aka kammala cikakken zama karo na 3 na kwamitin tsakiyar JKS na 18 a birnin Beijing, inda aka yi nazari aka kuma zartas da kudurin kwamitin tsakiya na JKS game da muhimman batutuwan da suka shafi zurfafa ayyukan yin kwaskwarima a gida a dukkan fannoni. Jama'a na ganin cewa, wannan muhimmin taro ne ga kasar Sin a kokarin da take yi bude wani sabon babi na yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje. A wannan rana, farfesa Xu ya yiwa 'yan jarida bayani game da sanarwar taron, cewa a fannin yin kwaskwarima kan tsarin siyasa, abin dake gaban kome shi ne tabbatar da yadda za a yi amfani da doka ba tare da boye kome ba, tare da bunkasa tsare-tsare a wannan fanni.
Dadin dadawa, farfesa Xu ya kara da cewa, cin hanci da rashawa wata babbar matsala ce, wadda za ta iya yin barazana ga JKS da kuma kasar Sin. Bisa sanarwar taron da aka bayar, an ce, za a mai da hankali kan matsalar ta hanyar amfani da iko, da fatan za a tabbatar da amfani da shi a bayyane yadda ya kamata kuma bisa tsari. Ban da haka, a gun cikakken zaman, an mai da hankali sosai kan bunkasa tsarin kasa, tare da dora muhimmanci sosai kan yaki da cin hanci da rashawa bisa tsarin dokar kasa. Da ma a kan gudanar da aikin yaki da cin hanci da rashawa a kai a kai, ba a jere ba. Yanzu kuma, za a yaki da matsalar ce bisa tsari, ba tare da kasala ba, wato bisa hanyar kimiyya.(Fatima)