Shugaban sashen nazarin harkokin hada-hadar kudi ta kwalejin nazarin kimiyyar zaman takewar al'ummar kasar Sin, Wang Guogang ya bayyana cewa, jaddada muhimmin tasirin kasuwa wajen rabon arziki, shi ne babban ci gaba da aka samu wajen yin kwaskwarimar tattalin arziki na wannan karo. Wang ya nuna cewa, a nan gaba, za a Baiwa kasuwa damar taka cikakkiyar rawa kan sanya farashi, kuma bai kamata gwamnati ta yi wa harkokin kasuwa tarnaki ba. A sa'i guda kuma bai dace a mayar da ayyukan gwamnati, tsarin harkokin siyasa da ikon mulki a kasuwa ba.
Bugu da kari, sanarwar kudurin zaman taron ta nuna cewa, kamata ya yi a daukaka ci gaba, da nasarorin da aka samu a manyan sassa, kana a bayar da tabbaci kan tattara ra'ayoyin jama'a game da manufar yin kwaskwarima. Game da wannan batu, Wang Guogang yana ganin cewa, bisa babban tsarin na kasa baki daya, ya dace a samu ci gaba a wasu fannoni wajen yi nkwaskwarima. Amma, hakan zai faru ne kawai idan an yi kwaskwarima, kan tsarin tattalin arziki tukuna. Amma rashin yin kwaskwarima kan zaman rayuwar al'umma, da al'adu, da siyasa, da yanayin muhalli, ba zai bari a iya ci gaba da yin kwaskwarima a tsarin tattalin arziki ba.
Wang ya kara da cewa, akwai bukatar a daga matsayin kwaskwarima a dukkan fannoni, matakin da aganinsa yake da matukar muhimmanci. (Bilkisu)