Kafofin watsa labaru na kasa da kasa da dama sun yi sharhi kan wannan batu, tare da bayyana gamsuwa ga kudurin da kwamitin na tsakiya na JKS ya gabatar, suna masu cewa, kuduri ne da ba a taba ganin irinsa a tarihi ba.
Har ila yau kafofin sun bayyana hanyar gurguzu da Sin ke bi, da cewa, hanya ce da ta dace a yi maraba da ita. Wannan takarda dai ta nuna cewa, matakan yin gyare-gyare da Sin za ta yi, ba a taba ganin irinsu a tarihi ba, za kuma su zama wata taswirar zurfafa yin gyare-gyare a dukkan fannoni.
Ra'ayin kasashen duniya kan wannan kuduri ya shafi bangarori masu yawan gaske, ciki hadda ra'ayin kamfanonin watsa labaru na AP da Reuters, da sauran manyan kafofin yada labaru. Kamfanin Reuters ya ce, wannan takarda ta shafi ayyukan yin gyare-gyare a fannoni da yawa. A sa'i daya kuma, jama'a daga sauran kasashe ciki har da Rasha, da Faransa, da Ingila, da New Zealand da dai sauransu sun tattauna kan kudurin da kwamitin tsakiya na JKS ya zartas.(Danladi)