in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasuwa na da muhimmanci sosai amma ba za ta iya daukar dukkanin nauyi ba
2013-11-15 14:18:33 cri

Shugaban kwalejin nazarin halin da kasar Sin ke ciki na jami'ar Tsinghua Hu Angang, ya zanta da manema labaru a ranar 12 ga wata a nan birnin Beijing, inda ya jadadda muhimmancin kasuwa, amma ya ce, wannan ba ya nuna cewa kasuwa na iya dauke dukkanin nauyi.

Da yammacin ranar kammalar cikakken zama na uku na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na sha takwas a birnin Beijing, an fidda sanarwar taron wadda ke cewa, yin kwaskwarima a fannin tattalin arziki ya kasance babban aiki cikin manufar zurfafa kwaskwarima da gwamnatin kasar Sin ke dauka, kuma muhimmin aiki da aka sa gaba shi ne, daidaita dangantakar dake tsakanin gwamnati da kasuwa, ta yadda kudade, ko kayayyaki za su rarrabu bisa tsarin kasuwa cikin inganci.

Har ila yau kamata ya yi a aiwatar da harkokin gwamnati cikin daidaici. Wannan ya kasance karo na farko, da gwamnatin kasar Sin ta gabatar cewa, kasuwa na da babban karfi a wannan fanni.

A ganin Hu Angang, bunkasuwar da aka samu a cikin shekaru 20 da suka gabata a fannin tsarin tattalin arzikin kasuwannin kasar Sin, ya zama wani mataki sabo a fannin manufofi, wanda kuma ya zo daidai lokacin da Sin ta kafa tsarin tattalin arzikin kasuwanninta na gurguzu. Ya zuwa yanzu, ana tabbatar da farashin kayayyaki, ko harkokin ba da hidima da yawansu ya kai kashi 95 bisa dari bisa dangantakar saye da sayarwa a kasuwa.

Ban da haka, Hu Angang ya nuna cewa, bisa shawarar da aka bayar yayin taron, ba ma kawai an ambaci amfanin kasuwa ba, an kuma tabo maganar tsarin daidaita harkokin tattalin arziki daga manyan fannoni da gwamnatin ke aiwatarwa. Wadanda suka zama bukatu na bunkasa tsarin tattalin arzikin kasuwannin kasar Sin na gurguzu, don haka ya kamata a yi amfani da su domin inganta zaman rayuwar jama'a. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China