Ban Ki-moon ya yaba da sakamakon da aka samu a yayin taron gamayyar kasa da kasa kan samun ci gaba ta IGAD da ya gudana a ranar 27 ga watan Disamba, da kuma ya kafa wata tawagar shiga tsakani domin yin aiki tare da gwamnati da kuma 'yan adawa na kasar Sudan ta Kudu ta yadda za'a tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu, da sakin fursunoni da kuma koma wa teburin shawarwarin neman sulhu, a cewar sanarwar da kakakin Ban Ki-moon ya gabatar.
A cikin wannan sanarwa, mista Ban ya yi alkawarin cewa MDD za ta tsaya kusa da al'ummar Sudan ta Kudu tare da ci gaba da kokarinta domin kare fararen hula da ba su taimakon jin kai.
Haka zalika sanarwar ta MDD ta kira da a kawo karshen duk wasu tashe tashen hankali, hare-hare da cin zarafin bil Adama ba tare da bata lokaci ba, sanarwar ta kara da dukkan mutanen dake da hannu kan wannan rikici za su gurfana gaban kuliya.
Ban Ki-moon ya kira ga gwamnati da bangarorin daban daban na kasar Sudan ta Kudu da wannan rikici ya shafa da su yi kokarin kare fararen hula da kare 'yancinsu.
IGAD, kungiyar shiyyar gabashin Afrika dake kunshe da kasashen Kenya, Sudan, Habasha, Djibouti, Somaliya, Uganda da Sudan ta Kudu za ta daukar wasu sabbin matakai idan har ba'a dakatar da wannnan rikici ba nan da kwanaki hudu masu zuwa, in ji shugabannin wannan kungiya. (Maman Ada)