in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikicin tsakanin sojojin Sudan ta Kudu da dakarun 'yan adawa da gwamnatin kasar ya ci gaba da tsananta
2013-12-30 15:31:09 cri
A ranar 29 ga wata, kafofin yada labaru na kasar Sudan ta Kudu sun bayyana cewa, sojojin gwamnatin dake karkashin shugabancin shugaban kasar Salva Kiir Mayardit da dakarun da ke adawa ga gwamnatin, wadanda ke goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar sun ci gaba da kai wa juna farmaki.

Kwanan baya shugaba Salva Kiir ya bayyana cewa, yanzu an dakile yarjejeniyar tsagaita bude wuta dake tsakanin bangarorin biyu, kuma mai yiwuwa ne, rikicin da ke tsakanin sojojin kasar da dakarun da ke adawa da gwamnatin zai ci gaba da tsananta.

A ranar 29 ga wata, bisa labarin da gidan rediyon kasar Sudan ta Kudu ya bayar, an ce, sojojin kasar Sudan ta Kudu za su yi shirin kai farmaki, don sake kwace birnin Bentiu da dakarun da ke adawa ga gwamnatin suka mamaye.

A sa'i daya kuma, kakakin sojojin kasar Sudan ta Kudu Pilip Aguer ya bayyana cewa, dakarun dake goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar su ma suna shirin kai farmaki, a yunkurin kwace birnin Bor hedkwatar jihar Jonglei daga hannun sojojin kasar. Ya ce, yanzu, rikicin dake tsakanin bangarorin biyu na ci gaba tsananta. Bisa labarin da wani gidan talibijin din kasar Sudan ya bayar, an ce, dubun dubantar magoyon bayan Machar sun taru a garin Bor.

A ranar 27 ga wata, a gun wani taron koli da aka shirya a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, an yanke shawarar kafa wani rukunin 'yan sulhu. Wannan rukuni zai yi kokari tare da gwamnatin Sudan ta Kudu da bangaren adawa na kasar, don daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakaninsu, don ba da tabbaci ga akin fursunoni 'yan siyasa da aka tsare a kasar, a yunkurin ingiza yin shawarwari a tsakanin bangarorin biyu. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China