Madam Hua ta ce tun barkewar rikicin a kasar ta Sudan ta kudu Sin na yin iyakacin kokarin ganin an samu zaman lafiya, inda ta sa kaimi don ganin an yi shawarwari tsakanin bangarorin biyu da rikicin ya shafa. Bugu da kari, Sin na shiga tsakanin bangarorin biyu ta bin hanyoyi daban-daban.
Ta yi bayanin cewa ya zuwa yanzu, wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin nahiyar Afrika jakada Zhong Jianhua ya bugawa ministan harkokin wajen kasar Sudan ta kudu waya, inda ya bayyana ra'ayin kasar Sin na neman bangarorin biyu da su yi hakuri da juna kuma daina yin amfani da karfin tuwo nan take sannan su koma teburin shawarwari.
Ganin yadda halin jin kai a kasar Sudan ta kudu ke kara tsananta, Madam Hua ta ce, Sin ta damu sosai a matsayin sahihiyar abokiyar kasar, kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta baiwa tallafin jin kai ga kasar dalilin zumunci dake tsakaninsu. Ban da haka, Sin za ta cigaba da baiwa kasar taimako gwargwadon karfinta nan gaba, tana mai kira ga kasashen duniya da su baiwa kasar Sudan ta kudu taimakon da ya dace. (Amina)