Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Zhang Ming ya gana da jakadun mambobin kungiyar raya gwamnatocin kasashen gabashin Afrika dake kasar Sin a ranar talata 24 ga wata a nan birnin Beijing, da suka hada da jakadun kasashen Sudan, Kenya da sauransu, inda Mr Wang ya yi kira ga bangarorin daban-daban da ke fuskantar tashin hankali a kasar Sudan ta kudu da su rungumi zaman lafiya.
Mr Zhang ya nuna cewa, Sin na mai da hankali sosai kan halin da ake ciki a Sudan ta kudu tare kuma da bayyana matukar damuwa kan rikicin da ya auku a kasar. Yana mai cewa, a matsayin sahihiyar abokiyar kasashen Afrika, Sin ta kan dauki matakin kiyaye zaman lafiya da karko a nahiyar, tare kuma da goyon bayan hanyar da jama'ar Afrika suka zaba wajen warware batutuwansu. (Amina)