Wannan ziyara na Shugaban kasar Sudan ta kudu din zai bude wani shafi na sabuwar dangantaka tsakanin Khartoum da Juba domin shawo kan duk wata matsalolin da suka addabe su wadanda ke kawo cikas ga dangantakar kasashen biyu,kamar yadda Ministan harkokin wajen Sudan Ali Karti ya bayyana ma manema labarai jim kadan da isar Kiir.
Ana sa ran lokacin ganawar Shugabannin biyu zasu tattauna dangantakar hadin gwiwa da kuma batutuwan da suka fi jawo hankalin kasashen su a bangaren man fetur,masana'antu,kudi,tsaro da kuma aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma tare.(Fatimah Jibril)