in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar MDD a Sudan ta kudu ta yi kiran da aka kwantar da hankali akai zuciya nesa.
2013-12-17 10:20:35 cri
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Sudan ta kudu wato UNMISS ta damu matuka dangane da fadan da ya auku a Juba, babban birnin kasar, in ji kakakin majalissar Martins Nesirky lokacin da yake bayani ga manema labarai a ranar Litinin din nan 16 ga wata.

Ya ce tawagar za ta cigaba da sa ido sosai da fatan ayyukan tsaro zai daidaita cikin sauri domin fararen hula su koma gidajen su.

Tawagar ta tabbatar da cewa, dubban al'umma sun nemi mafaka a harabar ofishin UNMISS dake daura da filin tashi da daukar jiragen sama da kuma ofishin majalissar dake Jebel Kujur tun lokacin da fada ya barke a daren Lahadi, kuma mafi yawan wadanda suka fake a nan mata ne da yara kanana.

Yanzu haka, ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na tawagar na cigaba da samar da ruwan sha da magunguna ga dubban wadanda suka tsere don neman mafaka a ofishin su a wuraren guda biyu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China