Kakakin sojojin Sudan ta kudu Philip Aguer ne ya sanar da hakan ga wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ta wayar tarho. Ya ce tun daga karfe 1 zuwa karfe 5 na yamma agogon wurin ne, dakarun SPLA da na Riek Machar suke ta gwabza fada,inda dakarun na SPLA suka yi galaba tare da tilasta musu ficewa daga inda suke.
Aguer ya kara nanata cewa, sojojin nasu a shirye suke su kwato Bantio, babban birnin jihar Unity mai arzikin mai wanda har yanzu ke hannun dakarun Machar.
Ya kuma tabbatar da cewa, fada ya barke ranar Talata a jihar Upper Nile da ke samar da galibin man kasar, tsakanin dakarun gwamnati da kungiyoyin dake dauke da makamai dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta kudu Riek Macha
A makon da ya gabata ne dai fada ya barke a kasar Sudan ta kudu tsakanin bangarorin sojojin biyu,wato kabilar Dinka ta shugaba Kiir, da kabilar Nuer ta Riek Machar, mutumin da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin Kiir.(Ibrahim)