in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan bangarorin daban-daban dake shafi batun nukiliyar kasar Iran ya shafa da su kai ga cimma matsayi daya tun da wuri
2014-01-21 20:44:26 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Hong Lei ya bayyana a nan birnin Beijing a talatar nan 21 ga wata cewa, Sin na fatan bangarorin daban-daban dake da alaka da batun nukiliyar kasar Iran su hada kai tare da nacewa ga yin shawarwari bisa daidaito, ta yadda za a kawar da bambancin ra'ayi da daidaita batun nukiliyar kasar Iran a dukkan fannoni cikin dogon lokaci.

Bisa labarin da aka bayar an ce, hukumar makamashin nukiliyar kasa da kasa IAEA ta tabbatar a ran 20 ga wata cewa, Iran ta fara aiwatatar da yarjejeniyar Geneva mataki na farko daga wannan rana, abin da ya hada da dakatar da tace sinadarin Uranium mai ingancin na kashi 20%. A nata bangare, Amurka ta yi maraba da wannan mataki, tare kuma da sanar da matakai da za ta bi a jere domin sassauta takunkumin da ta garkamawa kasar.

Dangane da batun, Hong Lei a lokacin da yake jawabi ga manema labaru a wannan rana ta talata 21 ga wata, ya bayyana cewa, a litinin din nan 20 ga wata, aka fara aiwatar da yarjejeniya a mataki na farko da kasashen shida da kasar Iran suka daddale a kan nukiliyar kasar Iran. Dagane da wannan Sin na jinjinawa kokarin da bangarorin daban-daban suka yi kan batun. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China