in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahalarta taron yin shawarwari kan batun nukiliya na Iran a Geneva sun ba da hadaddiyar sanarwa
2013-11-24 17:10:09 cri
A yau Lahadi 24 ga wata, babbar wakiliiyar kungiyar tarayyar kasashen Turai (EU) kan manufofin harkokin waje da na tsaro, Catherine Ashton ta gabatar da hadaddiyar sanarwa a madadin duk bangarorin da suka halarci taron yin shawarwari kan batun nukiliya na Iran, inda aka bayyana cewa, an cimma matsaya kan aikin daidaita batun nukiliya na Iran bayan yin shawarwari tsakaninsu.

Sanarwar ta ce, wannan yarjejeniya ta samar da wata hanyar da za a bi cikin dogon lokaci wajen tinkarar wannan batu. Bangarorin daban daban sun amince da daukar matakin farko na jurewa cikin watanni shida masu zuwa, a matsayin kashi na farko na yunkurin daidaita batun nukiliya na kasar Iran daga dukkan fannoni. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China