in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu ci gaba a yayin shawarwari game da batun nukiliya na Iran
2014-01-13 10:53:07 cri
A ranar 12 ga wata, babbar wakiliyar kula da harkokin diplomasiyya da manufofin tsaro ta kungiyar EU, Catherine Ashton, wadda ta yi shawarwari da kasar Iran kan batun nukiliya a madadin kasashen Amurka, Rasha, Sin, Faransa, Birtaniya, da Jamus, ta ba da wata sanarwa, inda ta bayyana cewa, kasa da kasa sun amince da yarjejeniyar da aka daddale tsakanin wadannan kasashe 6 da Iran kwanan baya a Geneva, kuma za a fara aiwatar da yarjejeniyar din ta wucin gadi a hukumance a ranar 20 ga wata.

Kasar Iran ta amince da sanarwar da Ashton ta bayar, kuma bisa wannan yarjejeniyar, Iran za ta dakatar da wasu ayyukan tace sinadarin Urunium cikin watanni 6 masu zuwa, don rage takunkumin da aka saka mata.

A ranar 12 ga wata, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ba da wata sanarwa, inda ya yi maraba da yarjejeniyar da aka daddale a wannan rana, game da batun nukiliya na kasar Iran a mataki na farko. Sanarwar ta ce, yayin da ake aiwatar da yarjejeniyar, kasashen duniya za su dauki sabbin matakai, don kara binciken batun nukiliya kan kasar Iran, idan kasar ta kasa cika alkawarin da ta dauka, to, za a maido da takunkumi a kasar nan take, kana za a kara sanya mata sabon takunkumi.

Kasashe 6 za su rage takunkumi da ka sanya Iran, yayin da takunkumi a fannin mai da hada-hadar kudi ke cigaba da aiki, amma za'a soke wasu takunkumin kan zinariya, da kera motoci, da aikin fitar da kayayyakin masa'antu a Iran. Ban da wannan kuma, a cikin watanni 6 masu zuwa, kasashe 6 da kasar Iran za su ci gaba da yin shawarwari, don daddale yarjejeniyar karshe, ta yadda za a warware batun nukiliya na kasar Iran daga duk fannoni, a sa'i daya kuma za a hana kasar samun makaman nukiliya, da ba da tabbaci ga kasar Iran wajen raya nukiliya na amfanin jama'a. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China