in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da bangaren adawa na Siriya sun yi maraba da soke gayyatar Iran shiga shawarwari kan batun Siriya da M.D.D. ta yi
2014-01-21 17:09:47 cri
A ranar 20 ga wata, sakatare janar na M.D.D. Ban Ki-moon ya soke gayyatar kasar Iran zuwa taron kasa da kasa game da batun kasar Siriya, goron gayyatar da bai kai awa 24 ba ya ba wa kasar.

A wannan rana, Ban ki-moon ya ba da wata sanarwa game da soke gayyatar Iran zuwa taron. Sanarwar ta ce, yayin da Ban Ki-moon ke tattaunawa da wani babban jami'in kasar Iran, jami'in ya dauki alkawarin nuna fahimta da goyon baya ga sharudan da aka samar game da gudanar da taron, cikinsu har da yarjejeniyar Geneva, alkawarin da daga bisani gwamnatin kasar Iran ta musunta, Ban ki-moon ya nuna takaici game da wannan, sabo da haka ne, ya sanar da yin watsi da goron gayyatar da ya ba wa Iran.

Ban ki-moon ya sanar da ba wa Iran goron gayyatar ne a gun taron manema labaru na M.D.D. da aka yi a ranar 19 ga wata da dare, abin da ya jawo hankalin jama'a, wanda kuma ya janyo rashin amincewa daga wajen Amurka da kuma Birtaniya da Faransa, wadanda suka bukaci Ban ki-moon ya sake yin la'akari da batun.

Babbar kungiyar adawa ta kasar Siriya ta ce, idan Iran ba ta nuna goyon baya ga gwamnatin wucin gadi ba, ba za su halarci taron ba.

Zaunannen wakilin kasar Iran a M.D.D. Mohammad Khazaee ya ce, idan aka gindaya sharadi ga kasar Iran game da halartar taron, Iran ba za ta amince da halartar taron ba.

A wannan rana, kakakin Ban ki-moon ya bayyana cewa, kafin Ban ki-moon ya aika da goron gayyata ga kasar Iran, bangarorin da abin ya shafa ciki har da Amurka sun san wannan batu, wato ke nan ba ta kawo cikas ba.

A ranar 20 ga wata da dare, babbar kungiyar adawa ta kasar Siriya ta yi maraba da soke gayyatar Iran zuwa taron da Ban ki-moon ya yi, kuma ya bayyana cewa, zai halarci taron da za a yi a wannan mako.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China