in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Iran ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin
2013-12-09 11:17:01 cri

A ranar Lahadi 8 ga wata, yayin da shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ke ganawa da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi, ya bayyana cewa, Iran tana fatan inganta mu'amala da hadin gwiwa da kasar Sin game da manyan batutuwan shiyya-shiyya.

Yang Jiechi ya bayyana cewa, kasar Sin tana sanya muhimmanci kan bunkasa dangantakar da ke tsakaninta da kasar Iran, kuma tana fatan kara daukaka dangantakar.

A nasa bangare kuma, Rouhani ya bayyana matsayin da Iran ke tsayawa game da batun nukiliya na kasar, inda ya sake jaddada shirin raya nukiliya na kasarsa domin zaman lafiya. Ya ce, kasar Iran tana fatan yin kokari tare da bangarorin da abin ya shafa, don tabbatar da yarjejeniyar da ta kulla tare da kasashe 6 ba tare da bata lokaci ba, da gaggauta share hanyar yin shawarwari na mataki mai zuwa. Kasar Iran ta yaba wa kasar Sin kan matsayi mai adalci da ta dauka da kuma kokarin sa kaimi ga n yin shawarwari, kuma tana fatan kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa game da batun.

Yang Jiechi ya bayyana cewa, kasar Sin tana girmamawa kasar Iran ikon yin amfani da makamashin nukiliya ta hanyar zaman lafiya na kasar Iran, kuma ya ce, ya kamata a lura da bukatar kasar Iran yadda ya kamata. Ya zama wajibi ga bangarori daban daban su warware batun nukiliya na kasar Iran ta hanyar yin shawarwari cikin zaman lafiya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China