Kakakin majalisar gudanarwa ta kasar Amurka Jen Psaki ta ba da wata sanarwa, inda ta nuna cewa, sakataren harkokin wajen kasar John Kerry ya riga ya amince da wasu matakan sassauta takunkumin da kasarsa ta kakaba wa kasar Iran, kuma zai sanar da majalisar dokokin kasar game da batun a wannan rana. Sa'an nan kuma, majalisar gudanarwa ta gabatar da cikkaken bayani kan yadda za ta sassauta takunkumin, da suka hada da amincewa da kamfanonin shida na kasar cigaba da sayan man fetur daga kasar Iran, bude wa Iran hanyar biyan kudaden harkokin jin kai, jinya, karatun daliban kasar dake ketare, zama mambar MDD.
Ban da wannan kuma, cikin watanni shida da kasar Iran zata gudanar da yarjejeniyar, Amurka za ta soke takunkumin kan kasar dangane da fitar da kayayyakin man fetur, karafa masu daraja da kuma takunkumin da ya shafi masana'antun motoci.
A ran 20 ga wata, hukumar makamashin nukiliyar kasa da kasa ta tabbatar da cewa, kasar Iran ta fara aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla yayin taron Geneva a mataki na farko, matakin ya hada da dakatar da aikin tace sinadarin uranium mai inganci, da kuma surka sinadarin uranium mai inganci da ta riga ta samu da sauransu.
A ran 24 ga watan Nuwamba na shakarar da ta gabata, kasar Iran da kasashen shida da batun nukiliyar kasar ya shafa sun cimma yarjejeniya ta makakin farko a yayin taron Geneva, inda kasar Iran ta yarda da dakatar da wasu ayyukanta game da nukiliya, muddin kasashem yammaci suka sassauta takunkumin da suka kakaba mata, sa'an nan kuma, a ran 12 ga watan da muke ciki, bangarorin da abin ya shafa sun cimma ra'ayi daya kan matakan da za a dauka don aiwatar da yarjejeniyar. (Maryam)