Amma ba a soke takunkumin da aka sanyawa kasar Iran a yanzu ba.
Ministan harkokin waje na kasar Faransa Laurent Fabius ya bayyana wa wakilin gidan rediyon Europe 1 na kasar a wannan rana cewa, kungiyar EU za ta dage wasu takunkumin da ta sanyawa kasar Iran a wata mai zuwa, amma an kayyade matakan soke takunkumin, kuma watakila za ta canja kudurinta na ci gaba da sanya takunkumin. Kana ya ce, ita ma kasar Amurka za ta dauki irin wannan mataki.
Ban da wannan kuma, ministan harkokin waje na kasar Canada John Baird ya sanar da cewa, kasarsa za ta ci gaba da sanya takunkumi kan kasar Iran a dukkan fannoni. (Zainab)