Ya ce, an cimma kaiwa ga daddale yarjejeniyar ce da Helga Schmid, mataimakin Catherine Ashton, shugabar kungiyar EU mai kula da harkokin diflomasiya da tsaro, bayan ganawar kwararru ta baya-bayan game da aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar da aka kammala a ranar Jumma'a.
Da zarar kasar ta Iran ta aiwatar da wannan yarjejeniya, kasashen 6, wato Amurka, Burtaniya, Faransa, Rasha, Sin da kuma Jamus za su yi kokarin ganin an fara sassauta takunkumin da aka kakabawa kasar ta Iran.
Jami'in kasar Iran din ya bayyana cewa, kasar a shirye take ta bar tawagar hukumar IAEA ta fara duba ko kasar ta Iran ta fara aiwatar da wannan yarjejeniya tun daga ranar 20 ga watan Janairu ko a'a. (Ibrahim Yaya)