Shugaba Rohani ya furta hakan ne a ranar Alhamis 5 ga watan nan a birnin Tehran hedkwatar kasar ta Iran, yayin ganawarsa da firaministan kasar Iraqi Nuri Kamal al-Maliki, wanda ke ziyarar aiki a kasar ta Iran.
Bisa sanarwar da wata kafar yanar gizo ta fitar, an ce yayin ganawar jagororin biyu shugaban kasar Iran ya bayyana bukatar inganta dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da Iraqi, tare da binciko hanyoyin cimma moriyar juna cikin dogon lokaci, musamman ma a fannin tattalin arziki, da samar da muhimman ababen more rayuwa.
Yayin da aka tabo batun kasar Siriya kuwa, shugaba Rohani ya ce ya kamata taron Geneva karo na 2 game da batun Siriya, wanda za a shirya nan ba da dadewa ba, ya taimakawa kasar wajen shirya babban zabe cikin 'yanci, kuma ba tare da gindaya wani sharadi ba.
A nasa tsokaci, Firaminista Maliki, ya bayyana farin cikin sa bisa nasarar da aka samu ta cimma matsaya guda a mataki na farko tsakanin Iran da kasashe 6 da batun nukiliyar ta ya shafa. Ya ce, ya yi imanin cewa, kokarin da gwamnatin Iran take yi, zai bada damar warware batutuwa na wannan yanki baki daya.(Bako)