in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fuskantar tafiyar hawainiya a shawarwarin da ake yi tsakanin kasar Iran da kasashe 6 da batun nukiliyar kasar ya shafa
2013-12-23 10:01:54 cri
A ranar 22 ga wata, a birnin Tehran babban birnin kasar Iran, ministan harkokin wajen kasar Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewa, ana fuskantar tafiyar hawainiya a shawarwarin da ke tsakanin kasar Iran da kasashe 6 da batun nukiliyar kasar ya shafa wato kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin, da Jamus.

A wannan rana, a gun taron manema labaru da aka shirya, bayan da Zarif ya gana da takwararsa ta kasar Italy Emma Bonino da ta kai ziyara a kasar, ya bayyana cewa, yanzu, Iran na yin shawarwari da kwararru na kasashe 6 daga dukkan fannoni, amma sabo da abubuwan da bangarorin biyu suka tattauna sun shafi abubuwa da dama, shi ya sa ake fuskantar tafiyar hawainiya wajen yin shawarwarin.

A wani bangare kuma, Zarif ya yi kira ga bangarorin biyu da su aiwatar da yarjejeniyar farko game da batun nukiliyar kasar ta Iran da aka daddale a birnin Geneva cikin tsanaki, kuma, yana fatan za a cimma matsaya guda a shawarwarin da aka fara. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China